
Sen. Saidu Muhammad Dansadau yana zubarda hawayensa akan abunda yake faruwa a Jihar Zamfara. Sannan Kuma ya umarce ni da na isar da sakon jajantawa akan Iftila’in da ya faru ga Al’ummar: JANGERU KWARE KURYA KURSASA BADARAWA ZANGEME GURBIN BORE KAURA SHINKAFI ZURMI TSAFE MARADUN Da Zamfara Baki Daya da sauran Kauyukan Zamfara wadanda Masifa da zubar da Jini Tare da Garkuwa da Mutane wadanda ta shafa. Wannan Masifa abar dubawa ce ya kamata Gwamnatin Jaha da Mahukunta su tashi tsaye domin ganin cewa an kawo karshen wannan masifa. Sen. Saidu Muhammad Dansadau yasha alwashin Idan Allah yasa yayi Nasara matsalar Tsaro ita ce Abu na Farko da zai Magance da Izinin Allah. Muna Fatan Allah yaba Sen. Saidu Muhammad Dansadau a Matsayin Gwamnan Jihar Zamfara 2019. Allah ya bamu zaman lafiya a Jihar mu da Kasa baki daya.
Programmers Association of Zamfara state 👨💻👩💻
Comments
Post a Comment