FAHIMTAR DA MUKA YIWA HALAYE DA KUDURORIN SEN. SAIDU MUHAMMAD DANSADAU
Bayan kammala nazari da bincike tare da tuntuba da neman shawarwari cewa a halin da siyasar jihar Zamfara take ciki a yau, babu wani mutum wanda ya cancanta da jagorancin jihar a 2019 don ceto al’ummar Zamfara sai Sen. Saidu Muhammad Dansadau, Gamji sha sassaka, gagara tarkon mahassada, sawun giwa badda na rakumi, bauna mai tafiyar kasaita, gugar karfe garnakaki, hadarin sama sai saurare, madugun nasara, sadauki, adili, mai gaskiya da rikon amana, haziki, jarumi, mai juriya, mai hikima, mai hakuri, mai son zaman lafiya, mai farin jini abokin kowa, gogaggen dan siyasa kuma masanin siyasar zamani, mai tausayin talakawa da kishin al’ummar jihar Zamfara, masanin makamar aiki, mai kyakkyawar manufa kuma dattijo a furucinsa da ayyukansa tare da dalilan da yasa muka zabe shi a matsayin wanda ya kamata mu mara wa baya domin cimma kuduroran da muka sanya wa gaba.
Sako Daga........
Programmers Association of Zamfara state π©π»π¨π»_
Comments
Post a Comment