'Dan takarar Gwamna a jam'iyyar NRM a jihar Zamfara, Sanata Sa'idu Dansadau ya bayyana cewa matukar suka shekara takwas kan mulki, to duk Dan jihar zamfara sai ya sami aikinyi.
'DanSadau ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da gangamin yakin Neman zabensa, da ya gabatar a garin Gusau ta jihar Zamfara.
Ya kara da cewa idan ka dubi Zamfara shekara Ashirin da suka wuce, sai ka zubda hawaye, saboda yadda zaka ga matasa suna yawo babu aikin yi, kuma ya ce mafiya yawansu duk sun yi karatun boko.
Dan takaran na Gwamna ya kara da cewa matukar al'ummar jihar zamfara suka zabi wannan Jam'iyya ta NRM, to kowane Dan zamfara sai ya sami aikinyi , kuma sai an dinga zuwa Kaduna ko Kano ana dauko ma'aikata saboda a basu aikinyi.
Da ya koma kan matsalar tsaro ya ce ya zama wajibi ga al'ummar jihar zamfara dasu fitone kwansu da kwarkwatansu don yakar Azzalumai, sabo da Allah baya son zalunci.
Ya ce kama daga Azzalumai masu kwashe kudin al'umma su fita dashi da Azzalumai masu kashe mutane suna kwashe masu dukiya da Azzalumai masu sace mutane don karbar kudin fansa da kuma Azzaluman da ke tai maka masu da labari , yace duk Allah ya la,ancesu.
Don haka ya zama wajibi ga al'umma su tashi su ya kesu don yakarsu jihadi ne kuma duk Wanda ya mutu kan wannan hanya ya yi shahada.
DanSadau ya bukaci jama'ar jihar zamfara su taho a tafi dasu cikin wannan jam'iyya mai Zuma na NRM, mai alamar kudan zuma.
Programmers Association of Zamfara State
Comments
Post a Comment