'Dan takarar Gwamna a jam'iyyar NRM a jihar Zamfara, Sanata Sa'idu Dansadau ya bayyana cewa matukar suka shekara takwas kan mulki, to duk Dan jihar zamfara sai ya sami aikinyi. 'DanSadau ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da gangamin yakin Neman zabensa, da ya gabatar a garin Gusau ta jihar Zamfara. Ya kara da cewa idan ka dubi Zamfara shekara Ashirin da suka wuce, sai ka zubda hawaye, saboda yadda zaka ga matasa suna yawo babu aikin yi, kuma ya ce mafiya yawansu duk sun yi karatun boko. Dan takaran na Gwamna ya kara da cewa matukar al'ummar jihar zamfara suka zabi wannan Jam'iyya ta NRM, to kowane Dan zamfara sai ya sami aikinyi , kuma sai an dinga zuwa Kaduna ko Kano ana dauko ma'aikata saboda a basu aikinyi. Da ya koma kan matsalar tsaro ya ce ya zama wajibi ga al'ummar jihar zamfara dasu fitone kwansu da kwarkwatansu don yakar Azzalumai, sabo da Allah baya son zalunci. Ya ce kama daga Azzalumai masu kwashe kudin al'umma...
In support of Sen. Saidu Muhammad Dansadau for Governor Zamfara State 2019 Insha Allah.
I already reserved my vote to you sir and equally compelled to convince and mobilize others to go for you. You're better than all of them as I once opportuned to witness your previous representation at senatorial race. You're most welcomed sir, just feel voted.
ReplyDelete